Isa ga babban shafi
Syria

‘Yan adawar Syria sun yi watsi da bukatun gwamnati

Yunkurin sasanta rikicin kasar Syria ya gamu da cikas bayan ‘Yan adawa sun yi watsi da bukatun gwamnatin Bashar Assad kafin cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta ta Kofi Anann mai shiga tsakanin rikicin kasar.

'Yan Tawayen kasar Syria masu yaki da gwamnatin Bashar Assad
'Yan Tawayen kasar Syria masu yaki da gwamnatin Bashar Assad Reuters
Talla

Hukumar kare hakkin bil’adama ta human Rights Watch tace Mutane 12 suka mutu a wani sabon rikici da ya barke tsakanin dakarun gwamnati da ‘Yan Tawaye a yankin Aleppo arewacin Syria.

Karkashin yarjajeniyar Kofi Annan, a ranar Talata ne aka bukaci dakarun gwamnati ficewa daga yankunan ‘Yan adawa domin kawo karshen Jubar da jinni a kasar.

Sai dai Gwamnatin Syria tace hakan ba zai samu ba sai idan ‘Yan Adawa sun tsagaita wuta.

Kwamandan ‘Yan Tawayen kasar, Kanal Riyadh yace sun amince da bukatun Kofi Annan amma ba zasu amince da bukatun gwamnatin Assad ba.

Masu sa ido a rikicin Syria, sun ce, mutane 51 suka mutu a ranar Lahadi bayan mutuwar wasu 130 a ranar Assabar.

A ranar Talata ne Kofi Annan zai kai ziyara kasar Turkiya, kafin ya kai ziyara kasar Iran aminiyar Syria, domin ganawa da ‘Yan gudun Hijira a kan iyakar Turkiya da Syria.

Gwamnatin China ta bukaci Syria amincewa da bukatun kasashen duniya domin kawo karshen zubar da jini a cikin kasar.

Majalisar dinkin duniya tace sama da mutane 9,000 ne aka kashe tun fara zanga-zangar adawa da gwamnatin Bashar Assad a watan Maris shekarar 2011.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.