Isra'ila-Felesdinu - 
Wallafa labari : Talata 07 Feberairu 2012 - Bugawa ta karshe : Talata 07 Feberairu 2012

Ban Ki-moon ya bukaci Abbas sasantawa da Isra’ila

Shugaban Falesdinawa Mahmoud Abbas
Shugaban Falesdinawa Mahmoud Abbas
REUTERS/Mohamad Torokman

Daga Awwal Ahmad Janyau

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban ki-moon, ya bukaci shugaban Falesdinawa mahmoud Abbas amincewa da ci gaba da zama a teburin sasantawa da Isra’ila bayan amincewa da shi matsayin shugaba a yarjejeniyar kawance tsakanin Fatah da Hamas.

Mista Ban wanda ya zanta da Abbas ta wayar Salula game da yarjejeniyar bangarorin Falesdinu a Qatar, ya bayyana fatar samun sulhu da Isra’ila.

A jiya Litinin ne kungiyoyin Hamas da fatah suka amince da Mahmud Abbas, a matsayin shugaba wanda zai jagoranci Gwamnatin rikon kwaryar da zata gudanar da zaben shugaban kasa da ‘Yan Majalisu bayan cim ma yarjejeniya tsakanin Abbas da Khaleed Meshaal.

Sai dai kuma Fira Ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya yi Allah waddai da wannan hadin kan Falasdinawa, a cewarsa kawance da Hamas mataki ne na kawo karshen sasantawa tsakanin Isla’ila da Falesdinu.

Amma Mista Ban ya jinjinawa sarki Abdallah na Jordan wanda ke kokarin shirya zauren sansatawa tsakanin Isra’ila da Falesdinawa a wannan watan.

 

tags: Isra'ila - Majalisar Dinkin Duniya - Yankunan Palasdinawa
KAN MAUDU'I GUDA
Ra'ayoyi
Bada ra'ayi kan wannan magana
The content of this field is kept private and will not be shown publicly.
To prevent automated spam submissions leave this field empty.
CAPTCHA
This question is for testing whether you are a human visitor and to prevent automated spam submissions.
Image CAPTCHA
Enter the characters (without spaces) shown in the image.
Close