Pakistan - 
Wallafa labari : Laraba 01 Feberairu 2012 - Bugawa ta karshe : Laraba 01 Feberairu 2012

Pakistan ta yi fushi kan rahoton NATO

Prime Ministan Pakisan Yusuf Raza Gilani
Prime Ministan Pakisan Yusuf Raza Gilani
REUTERS/Omar Sobhani

Daga Bashir Ibrahim Idris / Nasiruddeen Mohammed

KASAR Pakistan ta bayyana bacin ranta kan wani rahotan asiri na kungiyar kawancen tsaro ta NATO, wanda ya zargi jami’an tsaron kasar da taimakawa Yan kungiyar Taliban a kasar Afghanistan.
Rahotan wanda aka tsegunta wa manema labarai, yace Jami’an tsaron ISI na Pakistan na taimakawa Taliban a kasar Afghanistan, kamar yadda wasu shaidu 4,000 suka bada bahasi, yayin da ake yi musu tambayoyi.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Pakistan, Abdul Basit, yayi watsi da zargin, inda yake cewa su ba sa sanya hannu kan harkokin cikin gidan Afghanistan.
Wannan rahoto ya dada fito da zargin da Amurka da kasashen Yammacin duniya ke yiwa Pakistan, na jan kafa wajen yaki da ta’addanci, kamar yadda mai Magana da yawun ma’aikatar tsaron Amurka, Captain John Kirby ya bayyana.
Rahoton yace, Pakistan ta san inda shugabanin kungiyar Taliban suke, amma taki bada hadin kai, wajen sanar da kungiyar NATO domin kai musu hari.
Maimagana da yawun kungiyar NATO, Lt Col Jimmie Cummings, yaki cewa komai kan lamarin, inda yace rahotan na asiri ne, saboda haka bashi da hurumin Magana akai.
 

tags: Pakistan
KAN MAUDU'I GUDA
Ra'ayoyi
Bada ra'ayi kan wannan magana
The content of this field is kept private and will not be shown publicly.
To prevent automated spam submissions leave this field empty.
CAPTCHA
This question is for testing whether you are a human visitor and to prevent automated spam submissions.
Image CAPTCHA
Enter the characters (without spaces) shown in the image.
Close