Kasashen Larabawa - Wallafawa ta karshe : 11/01/12
Juyin-Juya halin Kasashen Larabawa
Daruruwan masu zanga-zanga a Dandalin Tahrir a birnin al Kahira na Masar

A ranar 18 ga watan Disemba ne aka fara kaddamar da zanga-zangar adawa da gwamnatocin kasashen Larabawa har zuwa yanzu. Domin neman girka gwamnatin Demokradiyya a kasashen Tunisia da Masar da Libya da Syria da Bahrain da Yemen da sauran kasashen Larabawa bayan kwashe tsawon shekaru shugabannin kasashen na gudanar da mulki sabanin na Demokradiyya.

An fara Zanga-zangar ne a kasar Tunisia inda ta yi sanadiyar hambarar da gwamnatin Zainul Abidina bn Ali, daga nan kuma zanga-zangar ta bazu zuwa kasar Masar da Libya inda ta yi sanadiyar kawo karshen mulkin Hosni Mubarak na Masar da Kanal Ghaddafi na Libya.

Mutane da dama sun rasa ransu saniyar zanga-zangar. A kasar Syria akalla sama da mutane 5,000 ne aka kashe, inda a kasar Libya fararen hula da dama suka mutu bayan shiga tsakanin kungiyar NATO domin taimakawa ‘Yan Tawaye.

 
Wani yana neman tsira da ranshi a wani hari da aka kai a Libya
14/05/2012 - Libya-NATO-HRW

NATO ta kashe fararen hula 72 a Libya, inji HRW

A wani Rahoton da Hukumar kare hakkin Dan adam ta Human Rights Watch ta fitar, rahoton yace a bara wani hari da kungiyar NATO ta kai ta sama ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula 72 a Libya, tare da zargin kawance kasashen Turai da suka kaddamar da yakin kawar da Gaddafi.

Kofi Annan a lokacin da yake jawabi a zauren Majalisar Dinkin Duniya game da Syria.
09/05/2012 - Syria-MDD

Annan yace tsarinsa na zaman Lafiya a Syria shi ne mataki na karshe

Jekadan Majalisar Dinkin Duniya na musamman a kasar Syria, Kofi Annan, ya shaidawa kwamitin Sulhu cewa, shirinsa na neman zaman lafiya shi ne mataki na karshe don kaucewa yakin basasa a kasar, a yayin da dakarun gwamati ke ci gaba da diran mikiya kan masu zanga zanga, da azabtar da fursunoni.

'Yan tawayen Libya rike da muggan makamai a lokacin yaki da dakarun Marigayi Gaddafi
09/05/2012 - Libya

An yi musayar Albarussai tsakanin ‘Yan bindiga da jami’an tsaron Libya

A kasar Libya mutane da dama sun samu rauni tare da samun mutuwar mutum daya sakamakon musayar wuta da aka yi tsakanin Jami’an tsaro da ‘Yan bindiga dwadanda suka yi zanga zanga a Hedikwatar Gwamnati a Birnin Tripoli.

Wani dan kasar Bahraini dauke da Tutar kasar a wani gangami da kungiyar adawa ta Wefaq suka hada a Bilad al-Qadeem, a yammacin  Manama
04/05/2012 - Bahrain

An yi wa Kundin tsarin Mulkin Bahrain kwaskwarima amma ‘Yan adawa basu amince ba

A kokarin shi na kawo karshen tashe tashen hankulan da ke faruwa a kasar Bahrain, Sarki Hamad ya amince da gyaran da aka yi wa tsarin mulkin kasar amma ‘Yan adawa sun nuna rashin amincewar su da karfin da aka kara wa majalisar kasar, inda suka ce bai isa ba.

Masu zanga-zanga a kasar Masar
03/05/2012 - Masar

Mutane 20 suka mutu a zanga-zangar kin jinin Sojin Masar

fiye da mutune 20 ne suka mutu a zanga-zangar kin jinin Soji da aka gudanar a birnin Alkahira na kasar Masar. Akan haka ne ‘Yan takarar shugabancin kasar 4 suka bayyana dakatar da gangaminsu sakamakon mutuwar mutanen.

Wani yankin birnin Homs da ake wa luguden wuta ya tirnike da hayaki.
26/04/2012 - Syria

Mutane 70 sun mutu a Syria sanadiyar wani hari da aka kai a Hama

‘Yan rajin tabbatar da Demokradiya a Syria sun ce Akalla mutane 70 suka mutu sanadiyar wani hari da aka kai a birnin Hama. Sun ce gidaje da dama ne suka kone musamman a yankin Mashaa at-tayyar bayan fashewar bama bamai.

Tsohon Fira Ministan Masar Ahmed Shafiq
25/04/2012 - Masar

Gwamnatin Sojin Masar ta haramta wa Jami’an Mubarak shiga zabe

Hukumomin Sojin kasar Masar, sun haramtawa Tsohon Fira Minista Ahmed Shafiq shiga takarar zabe, tare da jami’an da suka rike manyan mukamai a karakshin mulkin Tsohon shugaban kasa Hosni Mubarak, shekaru goma da suka gabata.

A lokacin rikicin kwallon kafa a filin wasan Pord Said tsakanin magoya bayan Al Masry da Al Ahly a Masar
24/04/2012 - Masar

An haramta gudanar da gasar kwallon kafa a Masar

Gwamnatin rikon kwarya a kasar Masar ta soke gudanar da duk wani wasan kwallon kafa a kasar. Hukumar kwallon kafar kasar tace akwai umurnin haramta gudanar da wasannin da suka samu daga ma’aikatar harakokin cikin gida, game da soke gasar lashe cin kofin Masar da aka shirya farawa a ranar 30 ga watan Afrilu.

Koffi Annan mai shiga tsakanin rikicin Syria a lokacin da yake ganawa da  Ban Ki Moon
20/04/2012 - MDD-Syria

Ban Ki-moon yace akwai Sarkakiya da fargaba a ziyarar masu sa ido Syria

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya yi kiran a gaggauta tura tawaggar sa ido don kawo karshen rikicin kasar Syrya, amma yace akwai sarkakiya da ban tsoro a ziyarar.

Tawagar 'Yan wasan Super Eagle
13/04/2012 - Kwallon Kafa

Masar ta doke Najeriya a wasan sada Zumunci

A kasar Daular Larabawa ‘yan wasan kasar Masar sun doke ‘yan wasan Najeriya ci 3-2 a wasan sada zumunci da aka gudanar a jiya. Stephen Keshi ne dai ya jagoranci ‘Yan wasan Super Eagle wadanda yawancin ‘yan wasa ne masu taka kwallo a gida Najeriya.

Ana ci gaba da Zanga-zanga kuma ana dakun Sakamakon zabe
DR. Suleiman Khali
 

Ana ci gaba da Zanga-zanga kuma ana dakun Sakamakon zabe. Dr Suleiman Khali Malami a Jami'ar Sokoto a Tarayyar Najeriya ya yi tsokaci akai

26/12/2011
by Nasiruddeen Mohammed
 
 
Saeed Ibrahim Inuwa Malamin Jami'ar Azhar
 
26/12/2011
 
 
Rikicin kasar Syria
Rikicin Syria: Dr Aliyu Tilde
 

Shugaban Kasar Syria, Bashar al Assad, ya musanta zargin da ake masa na sanya dakarun sa kashe masu zanga zanga. Aliyu Tlde ya yi tsokaci akai

26/12/2011
by Bashir Ibrahim Idris
 
 
Rikicin kasar Syria
Dr. Sadiq Alkafawi na Jami'ar Ahmadu Bello Zaria
 

Gwamnatin Assad ta amince da bukatar kungiyar Tarayyar Larabawa domin bada damar masu sa ido shiga kasar don kokarin sasantawa da kawo karshen Jubar da jini a cikin kasar

26/12/2011
by Garba Aliyu
 
 
Sabuwar gwamnatin Tunisia
Buhari Bello Cibiyar Binciken Siyasa a Afrika
 

An bukaci Fira Ministan kasar Tunisia kafa Gwamnati, Buhari Bello Cibiyar Binciken Siyasa a Afrika ya yi tsokaci akai

26/12/2011
by Nasiruddeen Mohammed
 
 
Rikicin kasar Syria
Mamman Sani Adamu Mai Sharhi kan Siyasar Duniya
 

An kai wani harin Bom a Birnin Hom na kasar syria inda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 30, a dai dai lokacin da wakilan kungiyar Larabawa zasu kai ziyara cikin kasar. Mamman Sani Adamu Mai Sharhi kan Siyasar Duniya a Jamhuriyyar Nijar ya yi tsokaci akai.

26/12/2011
by Salissou Hamissou
 
 
Zanga-zangar Dandalin Tahrir
Saeed Ibrahim Inuwa Malamin Jami'ar Azhar
 

Kasashen Duniya sun nuna bacin ransu ga yadda mahukuntar kasar ke murkushe masu zanga-zanga

26/12/2011
by Bashir Ibrahim Idris
 
 
Close