Asiya

Syndicate contentAsiya
Wata Zanga Zanga da Falesdinawa suka gudanar a Zirin Gaza domin neman sakin 'Yan uwansu da ake tsare dasu a Isra'ila
15/05/2012 - Falesdinawa-Isra'ila

Falesdinawa sun kawo karshen yajin cin Abinci a gidan yarin Isra’ila

Falesdinawa 1,500 da ke yajin cin abinci a gidan yarin Isra’ila, sun kawo karshen fafutukarsu, bayan kwashe sama da watanni biyu, saboda wata yarjejeniyar da aka kulla tsakanin Isra’ila da Falasdinu.

11/05/2012 - Pakistan-Indiya

Kasar Pakistan ta ce zata koma tuburin tattaunawa da Indiya dangane da tsaunin Siachen

A yau juma’a kasar Pakistan ta bayyana cewa a ranar 11 zuwa 12 ga watan yunin gobe ne, za a koma wata sabuwar tattaunawa tsakaninta da kasar Indiya dangane da tsaunukan Siachen, dake dankare ...

Tsaunin Salak na Indonesiya, da jirgin saman kasar Rasha ya fadi
11/05/2012 - Indonesiya

An fara neman gawarwakin wadanda suka mutu a hadarin jirgin Indonesiya

A kasar Indonesia, a yau juma’a masu aikin ceto, dauke da jikkunan zuba gawarwaki sun fara isa zuwa tsaunin nan da jirgin saman kasar Rasha, dauke da mutane 45 ya fadi.

10/05/2012 - Iraki

An gano gawwakin wasu mutane 7 dauke da harbin bindiga ga kai a kasar Iraki

Mahukumtan kasar Iraki sun bayyana cewa, a yau Alhamis sun gano gawwakin wasu mutane 7 da aka kashe ta hanyar harbin Bindiga a kai, bayan da aka daure masu hannuwa da idanu, a rairayin saharar yankin tsakkiyar kasar.

A Syriya wasu na dauke da gawar daya daga cikin mutanen da suka kone a wurin da aka kai harin a birnin Dams.10 mai 2012.
10/05/2012 - Syria

Akalla mutane 55 sun mutu, wasu 372 sun jikkata a wani harin kunar bakin wake a kasar Syriya

Akalla mutane 55 ne aka kashe a yayin da wasu sama da 372 suka jikkata a yau alhamis, sakamakon wasu hare-haren ta’addanci da aka kai da bam a birnin Damas babban birnin kasar Suriya, kamar yadda ministan cikin gidan kasar ya bayyana a wata sanarwa ta tashar talabijin din gwamnatin kasar.

Tariq al-Hashemi Matimakin Fira ministan Iraqi
08/05/2012 - Iraqi

Hukumar ‘Yan Sanda ta Duniya ta bukaci Cafke Mataimakin Fira Ministan Iraqi

Hukumar ‘Yan Sanda ta Duniya ta fitar da sanarwar bada umurnin Cafke Mataimakin Fira ministan Iraqi Tareq al-Hashemi wanda bisa zargin shi da taimakawa da bada tallafin kudi ga ayyukan ta’adanci.

Wani dan kasar Bahraini dauke da Tutar kasar a wani gangami da kungiyar adawa ta Wefaq suka hada a Bilad al-Qadeem, a yammacin  Manama
04/05/2012 - Bahrain

An yi wa Kundin tsarin Mulkin Bahrain kwaskwarima amma ‘Yan adawa basu amince ba

A kokarin shi na kawo karshen tashe tashen hankulan da ke faruwa a kasar Bahrain, Sarki Hamad ya amince da gyaran da aka yi wa tsarin mulkin kasar amma ‘Yan adawa sun nuna rashin amincewar su da karfin da aka kara wa majalisar kasar, inda suka ce bai isa ba.

cinkoson wasu fursunoni a cikin kaso
03/05/2012 - Isra'ila

Wasu Fursunonin Falastinawa 2 dake yajin kin cin abinci sun bayyana a gaban babbar kotun kasar Izra'ila

Wasu palastinawa 2 da kasar Izra’ila ke tsare da su, wadanda ke yajin kin cin abinci yau da kwanaki 65 da suka gabata, a yau alhamis sun bayyana a gaban madaukakiyar kotun kasar, wace ta sake duba bukatar da suka gabatar na neman a sake su, kamar yadda lauyan kungioyar kare hakkin dan adam ta palastinawa ya sanar a yau.

San Suu  na rantsuwar kama aiki a majalisar dokoki
02/05/2012 - Bama

Suu Kyi ta karbi rantsuwar kama aiki a Majalisar dokokin kasar

Jagorar yan adawar kasar Myanmar Uwargida Aung San Suu Kyi a yau ta yi rantsuwar kama aiki a matsayin wakiliyar Majalisar kasar, alamarin daya bude sabon babi a siyasar kasar.

yan sandan kwantar da tarzoma a unguwar  Abbassiyah, dake birnin Kairo na kasar Masar 30 avril, 2012.
02/05/2012 - Masar

Wata taho mu gama ta yi sanadiyar mutuwar mutane a kasar Masar

Akalla sama da mutane 10 ne aka kashe a yayinda wasu da dama suka jikkata a cikin wata taho mugamar da ta hada yan adawa da magoya bayan sozojin dake mulki, a kusa da ofishin ma’aikatar ministan tsaron kasar Masar

Un quartier de la ville d'Idlib, au nord de la Syrie, après deux explosions, le 30 avril 2012.
01/05/2012 - Syria-Tashin Hankali

An wayi gari cikin wani sabon tashin hankali a kasar Syriya, duk da kasancewar tawagar masu zura ido a kasar.

Kungiyar kare hakkin dan adam ta kasar Syriya ta bayyana cewa, a tashin hankalin na yau an kashe dakarun gwamnatin kasar Syriya 12,

Les familles des victimes du naufrage du ferry sur le fleuve Meghna, à 40 km au sud-est de Dacca, la capitale bangladaise, autour des corps retrouvés.
30/04/2012 - Indiya

wani jirgin ruwa dauke da mutane 250 ya nutse a kasar Indiya

A kasar India wani kwale-kwale dauke da mutane akalla 250 ya nutse a wani kogi, bayan wani mummunar iskar da ya taso, amma anyi katarin ceto mutane akalla 50.

Le quartier de Bab Dreeb à Homs, le 12 avril 2012.
30/04/2012 - Syria

Akalla dakarun gwamnatin kasar Syriya 20 ne suka rasa rayukansu a yau litanin

A yau litanin wasu hare-hare sun yi sanadiyar mutuwar mutane da dama mafiya yawansu kuma dakarun tsaron kasar Syriya a garin Ibleb dake yankin arewa maso yammacin kasar, kwana guda bayan isar janar Robet Mood shugaban tawagar masu zura ido MDD kan yarjejeniyar tsagaita buda wuta, a kasar ta Syriya inda tashe tashen hankulla suka yi sanadiyar mutuwar mutane 70 a wannan mako.

30/04/2012 - CHINA-USA

Chen Guang cheng mai kare hakkin dan adam din nan dan kasar China ya tsere a ofishin jakadancin Amruka

Dan gwagwarmayar kare hakkin dan adam din nan Chen Guangcheng da yayi nasarar tserewa daga gidansa inda mahukumtan China ke tsare da shi, yanzu haka ya na ofishin jakadancin kasar Amruka a birnin Pekin babban birnin kasar ta China, kamar yadda dan gwagwarmayar nan Hu Jian ya sanar, sai dai kuma ya ce bai nemi mafakar siyasa ba.

30/04/2012 - Iraki

an yi wa wata uwa da yayanta uku yankan rago a kasar Iraki

A tashe tashen hankullan da ke wakana a kasar Iraki, a yau litanin mutane 6 ne aka kashe a birnin Bagadad babban birnin kasar Iraki, mutanen da suka hada da wata uwa da yaranta 3, da aka kashe a gidansu ta hanyar daddaba masu wuka, kamar yadda majiyoyi masu kama da juna suka tabbatar.

Fira Ministan kasar Isra'ila Benjamin Netanyahu
30/04/2012 - Isra'ila

Benzion, Mahaifin Benjamin Netanyahu ya mutu yana da shekaru 102

Benzion Netanyahu, mahaifin fira ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya mutu a gidansa da safiyar litinin yana da shekaru 102 na haihuwa.

Matan Osama da 'Yayansa cikin wata motar Bus da aka samu hotun an dauko su daga Islamabad zuwa Filin zirgin sama da zai dauke su zuwa Saudiyya
27/04/2012 - Pakistan

Pakistan ta kori iyalan Osama zuwa Saudiya

Gwamnatin Pakistan ta kori iyalan marigayi Osama bin Laden zuwa Saudiyya da suka kunshi ‘Yayansa da matansa uku. Iyalan Osama sun kwashe lokaci suna zaune a Pakistan tun bayan da dakarun Amurka suka kashe shi a watan Mayun bara.

Wasu jami'an tsaron kasar Saudi Arbiya
26/04/2012 - Saudi Arabiya

kasar Saudiya ta zartar da hukuncin kisa kan wani mutum

Yau da safe a kasar Saudiyya aka fille kan wani mutun saboda laifin kisan kai a garin Asir dake kudu maso gabashin kasar.

Wani yankin birnin Homs da ake wa luguden wuta ya tirnike da hayaki.
26/04/2012 - Syria

Mutane 70 sun mutu a Syria sanadiyar wani hari da aka kai a Hama

‘Yan rajin tabbatar da Demokradiya a Syria sun ce Akalla mutane 70 suka mutu sanadiyar wani hari da aka kai a birnin Hama. Sun ce gidaje da dama ne suka kone musamman a yankin Mashaa at-tayyar bayan fashewar bama bamai.

Soldats yéménites à Sanaa le 1er mars 2012.
24/04/2012 - Yemen-Alka'ida

Sojan gwamnatin Yamen sun kusa kwace garin Zanjibar daga yan Alka'ida

 

Dakarun sojan kasar Yamen sun bayyana daukar sabin dubaru a yakin da suke yi da dakarun kungiyar Alka’ida tun farkon watan mayun 2011 da ta gabata a garin Zinjibar dake yankin kudancin kasar ta Yamen.

Close