Urgent published the Laraba 08 Feberairu 2012
Ahmadinejad zai gurfana a gaban Majalisar Iran
Majalisar Kasar Iran ta amince da kudirin aikewa da sammaci ga shugaba Mahmud Ahmadinejad, wanda shi ne irinsa na farko tun bayan juyin juya halin 1979. ‘Yan Majalisu 79 daga cikin 290 na Majalisar suka amince da kudirin, inda ake saran ya amsa tambayoyi kan tattalin arziki, da manufofinsa na cikin gida da na ketare.
Close