Isa ga babban shafi
Madagascar

‘Yan Majalisar Madagascar sun jefa kuri’ar tsige shugaban kasa

‘Yan Majalisar dokokin kasar Madagascar sun jefa kuri’ar tube shugaban kasar Hery Rajaonarimanpianina daga mukaminsa bisa zarginsa da taka kundin tsarin mulki da kuma nuna gazawa wajen tafiyar da mulki.

Shugaban Madagascar Hery Rajaonarimampianina
Shugaban Madagascar Hery Rajaonarimampianina REUTERS/Francois Lenoir
Talla

‘Yan majalisa 121 daga cikin 151 ne suka jefa kuri’ar amincewa da tsige shugaban wanda bai cika shekara guda ba akan karagar mulki, kuma a nan gaba kadan ne Kotun kolin kasar za ta bayyana matsayinta dangane da wannan mataki.

Ofishin jekadancin Amurka a Madagascar ya bukaci ‘Yan Majalisar su ba zaman lafiya muhimmaci a kasar tare da nuna goyon baya ga Rajaonarimanpianina.

Wasu ‘Yan Majalisar da ke goyon bayan shugaban sun yi zargin an yi magudi a kuri’ar tsige shi. Wasu sun ce adadin ‘Yan Majalisun ba su wuce 70 ba a zauren majalisar, a lokacin da aka kada kuri’ar.

A 2014 ne aka rantsar Rajaonarimanpianina a matsayin shugaban kasa, a karkashin wani tsari na kawo karshen rikicin siyasa a Madagascar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.