An ga Kasusuwa a gawar Sankara na Burkina
Kwararri da ke binciken musabbabin faruwar mutuwar tsohon shugaban kasar Burkina Faso Thomas Sankara, sun ce sun gano wasu kasusuwa da kuma wasu tsumma a cikin akwatin gawar da ake zaton ta marigayi Sankara ce da aka kashe ranar 15 ga watan oktoban 1987.
Wallafawa ranar:
Lauyan da ke kare iyalan marigayin, Benewende Stanislas Sankara, ya tabbatar da cewa an tarar da wadannan kasusuwa da kuma tsumma a akwatin, kuma za a yi bincike a kai domin tabbatar da musababbin mutuwar tsohon shugaban.
An kashe Sankara ne a juyin mulkin da ya ba Blaise Compaore nasarar darewa kan karagar mulki wanda aka hambarar da shi a 2014.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu