Isa ga babban shafi
ADB

Bankin raya Afrika zai zabi sabon shugaba

Bankin raya kasashen Afrika na ADB zai gudanar da babban taronsa karo na 50 inda za a zabi sabon shugaba a ranar Alhamis wanda zai gaji Donald Kaburuka na kasar Rwanda. Akinwumi Adesina na Najeriya yana cikin jerin ‘Yan takara da ke neman shugabancin Bankin.

Donald Kaberuka jagoran Bankin raya kasashen Afrika na ADB
Donald Kaberuka jagoran Bankin raya kasashen Afrika na ADB Jeune Afrique/Hassan Ouazzani
Talla

Kaberuka ya shafe shekaru 10 yana shugabancin Bankin wanda ya samar da ayyukan ci gaba da dama a karkashin jagorancinsa.

Akwai ‘Yan takara daga kasashen Saliyo da Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya da Guinea da kuma Dan Najeriya Akinwumi Adesina wanda kasashen Amurka da wasu na yammaci ke marawa baya.

Amma Faransa na neman ganin an zabi wanda ke ra’ayin manufofinta.

Dr Umar Mutallab Babban Jami’in gudanarwa Bankin musulunci na Jaiz a Najeriya ya zaben Adesina zai taimakawa Najeriya da Afrika wajen samar da ayyukan ci gaba a Nahiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.