Isa ga babban shafi
Najeriya

Bankunan Najeriya sun takaita ayyukansu saboda matsalar Mai

Wasu daga cikin Manyan bankunan Najeriya GT da Union sun bayar da sanarwar takaita ayyukansu a cibiyoyinsu da ke sassan Najeriya saboda matsalar karancin Mai da ke ci gaba da shafar harakokin kasuwanci a kasar.Bankin GT ya aika wa kwastamominsa da sako ta hanyar Email cewa zai takaita ayyukansa da misalin karfe 1 na rana tare da sake fitar da irin wannan sanarwa a shafin Twitter.

Wata Motar yaki ta 'Yan Sandan Najeriya kusa da masu zanga zangar tsadar Man fetir a Najeriya
Wata Motar yaki ta 'Yan Sandan Najeriya kusa da masu zanga zangar tsadar Man fetir a Najeriya REUTERS/Akintunde Akinleye
Talla

A nasa bangaren Bankin Union da ke da rassa sama da 300 a Najeriya ya fitar da sanarwa akan zai takaita ayyukansa zuwa karfe 2 na rana saboda matsalar karancin Mai.
Bankin GT da Unioin na daga cikin mayan Bankuna a Najeriya wadanda ke da yawan kwastamomi a kasar.

GT na da rassa a sassan Najeriya da kasashen yammaci da gabashin Afrika har zuwa Birtaniya.

Bankuna a Najeriya sun dogara ne da yin amfani da Janareto saboda matsalar karancin wutar Lantarki a Najeriya

Yanzu kuma Matsalar karancin Fetir ta dagula lamurra a Najeriya saboda sabani tsakanin Gwamnatin Goodluck Jonathan da Dillalan Man da kuma yajin aikin Ma’aikata da dirobobin tankokin Mai a kasar.

‘Yan Najeriya na sayen Litar mai Naira akan Naira 400 zuwa 500 musamman a kudancin kasar.

Matsalar ta kuma shafi kamfanonin sadarwa da suka hada da MTN da Airtel da Etisalat.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.