‘Yan Burundi na fama da Kwalera a Tanzania
Majalisar Dinkin Duniya tace kimanin mutanen kasar Burundi 3,000 ke fama da cutar Kwalera a sansaninsu na ‘Yan gudun hijira a Tanzania bayan sun tallaka kasar saboda rikici. Mahukuntan lafiya a Tanzania sun ce akalla mutane 33 suka mutu tun barkewar cutar a kauyukan Kogunga da Nyarugusu.
Wallafawa ranar:
Hukumar kula da ‘Yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya tace adadin na iya zarce haka, domin kimanin mutane 300 zuwa 400 ke kamuwa da cutar a kullum.
Majalisar Dinkin Duniya tace sama da ‘yan Burundi 100,000 suka fice kasar zuwa makwabta bayan barkewar zanga-zangar adawa da matakin shugaba Nkurunziza na neman wa’adin shugabanci na uku.
Hukumar ‘Yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya tace mutanen Burundi 70,200 suka tsere zuwa Tanzania, 26,300 suka tsallaka zuwa Rwanda, yayin da 10,000 suka shiga kudancin Kivu a kasar Jamhuriyyar Congo.
Yanzu haka 'Yan sanda na ci gaba da arangama da masu zanga-zanga a Burundi, lamarin da ke haifar da fargaba ga al'ummar kasar na yiyuwar barkewar yakin basasa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu