Mali
Dan bindiga ya bude wa Jami’an MDD wuta a Bamako
Wani dan bindiga ya bude wuta kan gidan da ma’aikatan Majalisar Dinkin Duniya suke zaune a Bamako, babban birnin kasar Mali. Dan bindigar ya harbi wani mai gadi farar hula, inda ya raunata shi, amma ba sojan da ya sami rauni a harin.
Wallafawa ranar:
Talla
Maharin ya yi ta harbin gidan, inda aka ajiye bindiga mai sarrafa kanta, kafin ya dana bom ya tsere.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Sojojin Faransa suka ce sun kashe kwamandojin mayakan jihadi, a yankin arewacin kasar, da ke fama da rikici
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu