An yi watsi da tuhumar kisa da ake yi wa Wasila
Masu gabatar da kara a Najeriya sun yi watsi da tuhumar kisa da ake yi wa Wasila Tasi’u ‘yar shekaru 15 kan zargin ta kashe Mijinta ta hanyar sa masa guba a abinci. Babban mai gabatar da kara Lamido Abba ya bukaci Kotun Gezawa a Kano ta yi watsi da shari’ar.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Wasila mai shekaru 14 a lokacin da aka daura mata aure da Malam Umar Sani, na kokarin kaucewa hukuncin kisa akan zargin ta kashe mijinta mai shekaru 35 da hanyar sa masa guba a Abinci.
Amma masu gabatar da kara na ganin Wasila da ta fito daga gidan Talakawa ta saka wa Mijinta guba ne saboda auren dole.
Al’amarin dai ya janyo mutuwar wasu mutane uku wadanda suka ci abincin da Wasila ta sanya wa Guba bayan an kammala bikinsu da Malam Umar.
Yanzu haka kotun ta dage shari'ar har zuwa 9 ga watan Yuni.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu