Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari : Kerry zai jagoranci tawagar Amurka a Najeriya

Fadar White House ta Amurka tace Sakataren harakokin waje John Kerry ne zai jagoranci tawagar kasar zuwa bikin rantsar da zababben shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a Abuja babban birnin Tarayya.

John Kerry Sakataren harakokin wajen Amurka
John Kerry Sakataren harakokin wajen Amurka REUTERS/Andrew Harnik/Pool
Talla

Fadar White House tace za ta bayyana adadin yawan Jami’anta da za su kawo ziyara a Najeriya nan da 'yan kwanaki masu zuwa.

A ranar 29 ga watan Mayu ne Muhammadu Buhari zai karbi rantsuwar kama aiki bayan ya kada shugaba mai barin gado Goodluck Jonathan a zaben da aka gudanar a watan Maris.

Akwai dai shugabannin Afrika da na kasashen yammaci da za su halarci bikin rantsar da Buhari a Najeriya.

Kerry ya taba kawo ziyara Najeriya a watan Janairu kafin a gudanar da zabe inda ya jaddada wa Muhammadu Buhari da Goodluck Jonathan game da matsayin karfafa huldar Amurka da Najeriya idan har an kammala zaben kasar cikin nasara.

Kasashen duniya da dama dai sun yaba da yadda aka gudanar da zaben Najeriya musamman ganin wannan ne karon farko da Jam’iyyar adawa ta kawar da Jam’iyya mai mulki a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.