Isa ga babban shafi
Burundi

Ana ci gaba da zanga zanga a Burundi duk da hukuncin kotu

A Kasar Burundi, mutane na ci gaba da zanga-zangar adawa da matakan zarcewa da mulki na Shugaba Pierre Nkurunziza, bayan da Kotun Kula da tsarin mulki ta wanke shi domin zarcewa da mulki wa’adi na uku

Masu zanga zangar adawa da matakin Shugaban Burundi na zarcewa da mulki
Masu zanga zangar adawa da matakin Shugaban Burundi na zarcewa da mulki REUTERS/Thomas Mukoya
Talla

Duk da cewar mataimakin shugaban kotun tsarin mulkin, yaki sanya hannu cikin shawarar da kotun ta yanke, kuma ya tsere ya bar kasar, wannan bai hana gabatar da matsayin kotun ba, da sauran alkalanta shida suka tsaida.

Masu bore dai sun ce, basu amince ba, kuma yanzu suka fara zanga-zangar nuna kyamar matakin.

Ta bangaren Gwamnatin dai, ta ce idan har sun jingine bore to kuwa za a sako wadanda ake tsare da su saboda shiga boren da aka kwashe sama da mako daya ana yi.

Kawo yanzu boren yayi sanadiyar mutuwar mutane akalla 13. Kuma mutane da dama sun jikkata, yayinda bayanai ke cewar jamian tsaro na tsare da mutane kusan 600.

 

 

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.