Isa ga babban shafi
Najeriya

An sake ceto Mata 160 a Sambisa

Rundunar sojin Najeriya tace ta sake ceto wasu Mata kimanin 160 wadanda ‘yan Boko Haram ke garkuwa da su a Dajin Sambisa, bayan an ceto kusan 293 a ranar Talata. Kanal Sani Usman ya ce kimanin Mata manya 60 aka ceto da ‘yan mata guda 100.

Labarin ceto 'Yan Mata kusan 300 a Sambisa ya mamaye kanun labaran jaridun Najeriya
Labarin ceto 'Yan Mata kusan 300 a Sambisa ya mamaye kanun labaran jaridun Najeriya REUTERS
Talla

Kanal Usman ya ce sun kwace tarin makamai daga hannun Boko Haram.

Jami’in ya ce ya zuwa yanzu sun lalata sansanin kungiyar Boko Haram 9 a Sambisa, amma an kashe soja guda da wata mace guda, yayin da sojoji 4 da wasu mata 8 suka samu raunuka dabam dabam.

Kanal Kukasheka ya bayyana sansanin da suka lalata da suka hada da Wulari Bukar, Gangala, Anguwar Bakwai da Jigide.

Sauran wuraren sun hada da Kotorima, da Lagara Bello da Lagara Fulani.

A ranar Talata ne Rundunar Sojin Najeriya ta ce dakarunta sun ceto ‘Yan mata kimanin 200 tare wasu manyan Mata guda 93 a dajin Sambisa sansanin mayakan Boko Haram da ke cikin Jihar Borno.

Amma har yanzu babu wani bayani daga rundunar sojin game tantance matan ko akwai ‘yan matan Chibok daga cikin wadanda aka ceto.

A ranar 14 ga watan Afrilu ne Mayakan Boko Haram suka yi awon gaba da ‘yan matan makarantar garin Chibok 276 a Jihar Borno. Ko da ya ke 57 daga cikinsu sun tsere daga hannun Mayakan.

A cikin wani hoton Bidiyo, shugaban Boko Haram Abubakar Shekau ya fito yana ikirarin cewa ya aurar da wasu daga cikin ‘yan matan Chibok tare da sayar da saura a kasuwar bayi.

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty Internetional tace kimanin mata 2000 ne mayakan Boko Haram suka sace tun bara.

Mutanen Jihar Borno da dama da aka sace ‘yayansu da ‘yan uwansu suna cikin zullumi tare da fatar ‘yan uwansu na cikin wadanda aka ceto.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.