Isa ga babban shafi
Nijar

Boko Haram ta kashe Sojojin Nijar da dama

Sojojin Nijar da dama ne mayakan Boko Haram na Najeriya suka kashe a gabar tabkin Chadi, kamar yadda wasu majiyoyin tsaro a Chadi suka tabbatar. Wannan na zuwa ne a yayin da mayakan suka abka cikin garin Karamga tare da yi wa fararen hula da dama yankan rago a ranar Assabar.

Kakakin rundunar Sojin Chadi Toma Hounou da ke fada da Mayakan Boko Haram na Najeriya
Kakakin rundunar Sojin Chadi Toma Hounou da ke fada da Mayakan Boko Haram na Najeriya
Talla

Wata Majiyar tace kimanin Sojojin Nijar 48 aka kashe, sannan 36 suka bace, amma wasu da dama sun samu tserewa.

Amma Wata majiyar tsaron daga yankin Diffa da ke kan iyaka da Najeriya ta tabbatarwa kamfanin dillacin Labaran Faransa cewa adadin Sojojin da aka kashe sun kai 80, yayin da 30 daga cikinsu bas an inda suka shiga ba.

Majiyar ta kuma ce Sojoji biyar ne kacal suka tsere.

Rahotanni daga Diffa na cewa adadin Sojoji 150 Nijar ta tura a yankin tabkin Chadi inda mayakan Boko Haram suka kai hari.

Tun a ranar Assabar ne rahotanni suka ce ‘yan Boko Haram suka shiga garin Karamga inda suka kona ‘yan gudun hijira da dama da ransu.

Zuwa yanzu dai babu wani bayani da ya fito daga bangaren rundunar sojin Nijar game da harin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.