Isa ga babban shafi
Burundi

Ana zanga-zangar kin jinin Nkurunziza a Burundi

‘Yan sanda a kasar Burundi sun yi arangama da masu zanga-zangar adawa da shugaban kasar Pierre Nkurunziza wanda ya ayyana neman wa’adi na uku a kan madafan ikon kasar. Rahotanni sun ce hukumomin kasar sun rufe babbar tashar rediyo a yayin da ‘Yan adawa ke ci gaba da zanga-zanga a sassan Burundi.

Wasu daga cikin masu zanga-zanga  a birnin bujumbura
Wasu daga cikin masu zanga-zanga a birnin bujumbura REUTERS/Thomas Mukoya
Talla

Kwana biyu ke nan aka shiga ana gudanar da zanga-zangar adawa da matakin shugaban Burundi na neman wa’adi na uku akan karagar mulki.

Rahotanni daga Burundi na cewa mahukuntan kasar sun cafke Pierre-Claver dan raji kare hakkin bil’adama tare da bayar da sammacin cafko masu jagorantar zanga-zangar neman haramtawa Pierre Nkurunziza yin tazarce.

Akalla mutane 5 aka ruwaito sun mutu bayan da ‘yan sanda suka budewa masu zanga-zanga wuta a Bujumbura babban birnin Burundi.

Yanzu haka kuma an baza jami’an tsaro a sassan birnin domin tunkarar masu zanga –zanga.

Zanga-zangar dai ta barke ne a Burundi a ranar Lahadi bayan Jam’iyyar CNDD mai mulki ta ba shugaban kasa Nkurunziza damar neman wa’adi na uku a zaben shugaban kasa da za a gudanar a ranar 26 ga watan Yuni.

Kuma tun a 2005 ne shugaban ke jagorantar kasar, yayin da ‘yan adawa ke bayyana cewa matakin tazarcen ya sabawa kundin tsarin mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.