Isa ga babban shafi
Togo

Ana zaben shugaban kasa a Togo

Alummar kasar Togo na zaben shugaban kasa yau asabar inda shugaba mai ci Faure Gnassingbe ke neman zarcewa da mulki wa'adi na uku da zai baiwa iyalan gidansu  zama a madafun ikon kasar na tsawon  kusan shekaru 50.Bayanai daga Lome na cewa mutane sun fito a wasu sassan kasar domin tafiya rumfunar zabe.Akwai 'yan sanda kusan dubu tara da wasu sojoji dake sintiri a koina cikin kasar.Hukumomin kasar sun rufe kan iyakoki domin gudun kada ayi masu kutse.Shugaban kasar mai ci Faure Gnassingbe mai shekaru 48 ya maye gulbin mahaifin sa ne da ya mutu tun shekara ta 2005.

Layin mutane na jiran su jefa kuria a Lome, Togo.
Layin mutane na jiran su jefa kuria a Lome, Togo. RFI / O.R.
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.