Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Ana gangami kyamar baki a Afrika ta Kudu

A Kasar Afrika ta kudu, Dubban jama’a ne suka shirya tsaf domin gudanar da zanga zanga a birnin Johannesburg a yau, da nufin nuna rashin amincewarsu game da hare haren da a ke ci gaba da kai wa bakin kasashen ketere da ke ci rani a Kasar

Bakin da ke fuskantar barazar rikicin kiyayya a Afrika ta kudu
Bakin da ke fuskantar barazar rikicin kiyayya a Afrika ta kudu REUTERS/Siphiwe Sibeko
Talla

Wanann na zuwa ne bayan jami’an tsaro daya hada da ‘Yan sanda da Sojoji sun kaddamar da samame a mobayar ‘Yan daban dake jan ragama wajan kai wa bakin hari, kuma sun yi nasarar cafke muta ne biyu.

A wannan makon ne hukumomin suka tura Sojoji domin taimakawa jami’an ‘Yan sanda a aikinsu na kama wadanda a ke zargi da kai farmaki ga bakin da suka shigo Afrika ta kudu daga kasashen Zimbabwe da Malawi da Mozambique da sauran kasashen yankin Afrika.

Akalla mutane 6 ne suka rasa rayukansu a harin na nuna kiyayya ga bakin kasashen ketare, inda ‘Yan Afrika ta kudun ke zargin su da mamaye ayyukan yi da Kasuwanci a Kasar.

A shekara ta 2008, irin wannan al-amarin ya faru a Afrika ta kudu, inda mutane 62 suka rasa rayukansu kuma akasarinsu a birnin Johannesburg aka kashe su.

A ranar larabar data gabata ne Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon ya yi tur da harin kuma ya yi kira bisa dau mataki don hana aukuwar haka nan gaba.

A dayan bangaren, Shugaba Jacob Zuma ya lashi takobin magance matsalar kin baki a Kasarsa, inda yace, matukar gwamanati bata dau matakin da ya dace ba, lallai da yiwuwar sake faruwan lamarin nan gaba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.