Isa ga babban shafi
Sudan

Sudan ta zargi Kasashen Turai da tsoma baki a harkar Zabe

Gwamnatin Kasar Sudan ta kira jakadun kasashen Birataniya da Norway da Amurka sakamakon furucin da suka yi, na sukar yadda aka gudanar da zaben shugajbancin kasar a makon da ya gabata

Shugaban kasar Sudan Umar Hassan Al Bashir, lokacin da ya ke kada kuri'arsa.
Shugaban kasar Sudan Umar Hassan Al Bashir, lokacin da ya ke kada kuri'arsa. REUTERS
Talla

A ranar litinin ne, kasashen uku suka bayyana takaicinsu bisa gazawar gwamnatin Sudan dangane da samar da kyakkyawan yanayi da zai kai ga gudanar da ingantaccen zabe.

Ma’aikatar harkokin wajen Sudan ta zanta da Kasashen, inda ta zarge su da sukar kasar tare tsoma baki akan lamarin da bai shafe su ba.

A dayan bangaren kuwa, gabanin fara zaben ne, Shugabar harkokin wajen Kungiyar nahiyar turai, Federica Mogherini ta bayyana cewa, mawuyaci ne a gudanar da ingantaccen zabe a Sudan, da jama’a zasu yi na’am da sakamakon.

Kimanin ‘yan takara 13 ne suka jajirce wajan kalubalantar Shugaba Omar Al-Bashir bayan ‘yan takara biyu sun janye, inda suka yi korafi tare da bayyana rashin gamsuwarsu game da zaben yayin da ake sa ran cewa, nanda mako mai zuwa za a sanar da sakkamakon zaben.

Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya na neman Shugaba Bashir sakamaon zargin sa da aikata laifukan yaki da kuma cin zarafin bil- Adama daya hada da kisan kare dangi a yankin yammacin Darfur.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.