Isa ga babban shafi
Saliyo-Ebola

Masu dauke da Ebola sun tsere a Saliyo

‘Yan Sanda a kasar Saliyo sun kaddamar da bincike dan gano wasu masu fama da cutar ebola da suka tsere daga inda aka aje su ake kula da su, bayan daya daga cikin su ya mutu.Cibiyar kula da masu fama da cutar ta ebola a Saliyo ta sanar da cewar mutane 7 suka tsere daga inda aka kille su dan basu magani, lokacin da daya daga cikin masu fama da cutar a Moa Wharf ya rasu.

Masu kula da mutane dauke da Ebola a Saliyo
Masu kula da mutane dauke da Ebola a Saliyo REUTERS/James Giahyue
Talla

Cibiyar tace mutanen 7 duk sun fito ne daga gida guda, cikin su harda mahaifiyar su, saboda haka hukumomin kasar suka bukaci taka tsan tsan wajen mu’amala da su.

A wani labarai kuma, Cibiyar ta sanar da killace wasu mutane 6 da suka yi mu’amala da wani mai fama da cutar dan ganin an basu kula ta musamman.

Cutar ebola ta kasha mutane sama da 1,000 a kasar ta Saliyo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.