Isa ga babban shafi
Masar

Kotun Masar ta daure Morsi shekaru 20

Kotun kasar Masar ta yankewa hambararen shugaba Mohammed Morsi hukuncin daurin shekaru 20 a gidan yari kan tuhumar da ake ma sa na tinzira jama’a a tashin hankali da ya faru a zamanin mulkinsa a 2012 a cikin kasar. Amma kotun ta wanke Morsi daga tuhumar kisan masu zanga-zanga wanda zai kai a yanke masa hukuncin kisa.

Kotun Masar ta wanke Morsi daga laifin kisan masu zanga-zanga bayan ta yanke masa hukuncin daurin shekaru 20
Kotun Masar ta wanke Morsi daga laifin kisan masu zanga-zanga bayan ta yanke masa hukuncin daurin shekaru 20 REUTERS
Talla

Kotun ta yanke wa hambararren shugaban Mohammed Morsi hukuncin daurin shekaru 20 akan laifin bayar da umurnin a kame masu zanga-zanga tare da gana masu azaba a lokacin da ake zanga-zangar kin jinin gwamnatinsa a 2012.

Baya ga Morsi Akwai kuma wasu mutane 14 da kotun ta yanke wa hukunci.

Sai dai kuma kotun ta wanke morsi daga laifin da ya shafi bayar da umurnin kisan masu zanga-zanga, wanda zai kai ga yanke masa hukuncin kisa.

Sannan kotun kuma na zarginsa da mika bayanan sirrin gwamnati ga kungiyar Hamas ta Falasdinawa, zargin da zai sa a sake yanke masa wani hukunci

Morsi dai shi ne zababben shugaban kasa na farko a Masar wanda ya gaji gwamnatin Hosni Mubarak da aka hambarar da gwamnatinsa a 2011.

Yanzu haka kungiyar ‘yan uwa musulmi ta kira babbar zanga-zanga domin nuna goyon baya ga Morsi.

Morsi na da ‘yancin daukaka kara bayan kotun ta yanke masa hukunci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.