Isa ga babban shafi
Algeria-Faransa

An cika shekaru 70 da Faransawa suka hallaka dubban 'yan Aljeriya

Jiya Lahadi tsofaffin Ministocin kasar Faransa sun kai ziyara kasar Algeriya, saboda cika shekaru 70 da wani tashin hankalin da yayi sanadiyyar kisan ‘yan kasar ta Algeriya da suka kai dubu 45. Turawan mulkin Mallaka da dakarun Faransa ne suka aiwatar da Kisan na shekarar 1945.Daya daga cikin jami’an gwamnatin Faransa da suka kai ziyarar Jean-Marc Todeschini yace, ziyarar wani mataki ne dake nuna cewa Faransa ta damu da wahalar da lamarin ya jefa ‘yan kasar ta Algeria.Kashe kashen sun faro ne daga kasuwar garin Sétif, bayan wata zanga zangar da aka yi a ranar 8 ga wata Mayun shekarar 1945, kashe garin ranar da aka kawo karshen yakin duniya na 2 a Nahiyar Turai.Zanga zangar ta kunshi ‘yan gwagwarmayar samun ‘yancin kai, wadanda kame Tutocinsu da na kasar Aljeria, da a lokacin aka haramta su, da jami’an ‘yan Sanda suka yi, ya haifar da musayar wuta.Kwanaki 5 bayan tashe tashen hankulan sai Soja da ‘yan sandan Faransa, da ma fararen hula ‘yan mulkin Mallaka suka fara daukar fansa, inda suka yi ta kashe ‘yan Aljeriya da ake zargi suna da hannu, a wasu lokutan kuma suka yi ta dasa bama bamai a kauyuka.Hukumomin Faransa a wancan lokacin sun kiyasta cewa mutane dubu 1 da ‘yan kai ne suka mutu, sai dai gwamnatin Aljeriya ta dage kan cewa mutane dubu 45 aka hallaka. 

Shugaban kasar Algeria, Abdoulaziz Bouteflika
Shugaban kasar Algeria, Abdoulaziz Bouteflika english.ahram.org.eg
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.