Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Shugaban Africa ta Kudu ya dakatar da ziyarar da ya shirya kaiwa Indonesiya

Shugaban kasar Africa ta Kudu Jocob Zuma ya dakatar da ziyarar da ya shirya kaiwa kasar Indonesia, don ya samu damar shawo kan tashe tashen hankulan da keda alaka da kisan ‘yan kasashen waje a kasar. Wannan matakin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da bayyana damuwa a cikin kasar, yayin da kasashen ketare ke ci gaba da Allah wadai da kashe kashen da ake yi.A nashi bangaren shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe ya bayyan takaici kan kashe kashen na Africa ta Kudu.Bayanai na cewa wasu ‘yan kabilar Zulu sun kone baki kimanin 6 a birnin Durban.A daren jiya juma’a kawai, an kama fiye da mutane 30, da ake zargin suna da hannu cikin lamarin, a kusa da birnin Johannesburg. 

Shugaban Africa ta Kudu Jacob Zuma
Shugaban Africa ta Kudu Jacob Zuma Reuters/Nic Bothma/Pool
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.