Isa ga babban shafi
Afrika ta Tsakiya-Kenya

Kenya na neman sassanta rikicin Afrika ta tsakiya

A yau talata a birnin Nairobi na kasar kenya Manyan masu rikici da juna a kasar Jamhuriya Afrika ta Tsakiya, tsofin yan tawayen Seleka da dakarun sa kai na Anti Balaka, na ci gaba da kokarin inganta yar ranke ranken yarjejeniyar zaman lafiya da suka cimma a watannin da suka gabata, karkashin shiga tsakanin kasar Kenya.

Wasu yan kungiyar Anti Balaka a kasar Afrika ta Tsakiya
Wasu yan kungiyar Anti Balaka a kasar Afrika ta Tsakiya © Michaël Zumstein / Agence VU pour Le Monde
Talla

Rikici tsakanin yan tawayen kungiyar Saleka da akasarin su musulmi ne da mayakan sa kai Anti Balaka kiristoci ya gagara karewa a kasar ta Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya duk da kasancewar dakarun MDD da Faransa da na kasashen Afrika na ta kokarin ganin kwanciyar hankali da zaman lumana sun samu gindin zama a kasar da ta share sama da shekaru 30 ta fama da rikici.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.