Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya yaba wa Jonathan

Sabon zababben shugaban Najeriya Janar Muhammadu Buhari ya yaba wa shugaba mai bari gado Goodluck Jonathan akan dattakun da ya nuna na amincewa da sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar Assabar tare da taya shi murnan lashe zaben.

Yarjejeniyar amincewa da matakin kaucewa rikici tsakanin Goodluck Jonathan da Janar Muhammadu Buhari a zaben 2015.
Yarjejeniyar amincewa da matakin kaucewa rikici tsakanin Goodluck Jonathan da Janar Muhammadu Buhari a zaben 2015. Reuters
Talla

“Da misalin karfe 5 na yamma, shugaba Jonathan ya kira ni tare da taya ni murnar nasarar lashe zabe” inji Buhari, bayan hukumar zabe ta sanar da shi a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa.

Buhari ya yi kira ga ‘Yan Najeriya su yaba wa Jonathan ga irin dattakun day a nuna na amincewa da shan kaye tun kafin a bayyana sakamakon zabe.

Buhari ya lashe zaben ne da rinjayen kuri’u Miliyan 2.57 tsakanin shi da shugaba mai ci Goodluck Jonathan.

Wannan ne kuma karo na farko da Shugaba mai ci ya sha kaye a tarihin siyasar Najeriya.

A jawabin da ya yi ta kafofin yada labaran Najeriya, Goodluck Jonathan ya shaidawa al’ummar kasar cewar ya cika alkawarin da ya yi na gudanar da karbabben zaben da duniya ta amince da shi.

Shugaban mai barin gado ya mika godiya ga daukacin ‘Yan Najeriya akan damar da suka ba shi na jagorantar Najeriya.

Masu sharhi dai na ganin kalaman Jonathan a matsayin babbar nasara ga ci gaban dimokuradiya a Najeriya.

Matakin da Goodluck ya bi ya samu yabo daga sassa dabam dabam na al'ummar kasar da kuma kasahsen duniya.

Abubuwa da dama ne dai suka yi sanadin faduwar gwamnatin Jam'iyyar  PDP ta Goodluck Jonathan da suka hada da tabarbarewar tsaro da tattalin arziki da matsalar cin hanci da rashawa da rashin ayyukan yi tsakanin 'Yan Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.