Buhari na kan gaba a zaben Najeriya
Dan takarar Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari na Jam’iyyar APC mai adawa ne a kan gaba a sakamakon zaben shugaban kasa na Jihohi 18 da Abuja da hukumar zaben Najeriya ta sanar, inda ya ba shugaba Goodluck Jonathan tazarar kuri’u sama da Miliyan biyu.
Wallafawa ranar:
Buhari na Jam’iyyar APC ya lashe Jihohi 10, yayin da Jonathan na PDP ya lashe 8 hadi da birnin Tarayya Abuja, a sakamakon da hukumar zaben kasar ta sanar na Jihohi 18.
Sai da misalin karfe 10 na safiyar Talata ne za a ci gaba da bayyana sakamakon zaben a sauran Jihohi 18.
Zuwa yanzu Buhari ya samu kuri’u Miliyan 8.5, tazarar kuri’a Miliyan biyu tsakanin shi da Jonathan. Amma cikin manyan Jihohin da ba a bayyana ba akwai Lagos da Jihar Rivers masu yawan kuri’u.
Buhari ya samu Kuri’u da yawa a Jihohin Kano da Katsina da Kaduna da Jigawa da Oyo da Kwara da Kogi da Ondo da Osun da Ogun.
Jonathan ya samu Kuri’u a Jihohin Ekiti da Enugu da Nasarawa da Abia da Imo da Abuja da Akwa Ibom da Filato da Anambra.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu