Isa ga babban shafi
Ebola

MDD bata gamsu da yadda ake yaki da Ebola ba a duniya

Jagoran tawagar masu yaki da Cutar Ebola ta Majalisar Dinkin Duniya Isma’il Ould Shaikh, ya koka kan abin da ya kira rashin gamsuwa da nasarorin da ake cewar suna samu, dangane da yadda suka gudanar da aikin yakar Cutar a kasashen duniya. Sai dai shugaban ya kuma yabawa kasar Guinea kan yadda ta kara matsa kaimi wajen takaita yaduwar Cutar.Kafin wadanan kalaman na Isma’il Shaikh, Hukumar lafiya ta Duniya WHO, ta fitar da Rahoton cewar yanzu dai an saka wa Cutar ta Ebola wakafi a yankin Nahiyar Africa ta yamma, bayan samun labarin cewa kassahe 3 da Cutar ta addaba a baya wato Liberia, Saliyo da Guinea, sun wayi gari babu mai dauke da Cutar a cikinsu.Haka ma Kalaman na Isma’il Ould Shaikh sun fito ne bayan da haka kwatsam! Suka ji labarin cewar kasar Guinea ta ayyana shirin ko-ta-kwana a yankunan kudancin kasar 5, da kuma wani yanki na yammacin kasar har na tsawon kwanaki 45.Yanzu haka dai an rufe wasu cibiyoyin kiyon lafiya da assibitoci a kasar ta Guinea, saboda fargabar yaduwar Cutar zuwa wasu wuraren da a daa, bata kai ba.Tun bayan da aka fara samun barkewar Cutar Ebola a kasar ta Guinea a cikin Watan Disamban 2013, akalla mutane Dubu 24 ne suka kamu da ita cikin hanzari a cikin kassahe 9, a yain da sama ga dubu 10 kuma suka mutu, akasarinsu kuma daga kasashen Liberia, da Sierra Leone da Guinea. 

Shugaban tawaggar yaki da cutar Ebola ta MDD, Ismail Ould Sheikh Ahmed
Shugaban tawaggar yaki da cutar Ebola ta MDD, Ismail Ould Sheikh Ahmed unicnetwork.org
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.