Isa ga babban shafi
Nijeriya

AU da ECOWAS sun yaba da zaben Najeriya

Tawagar masu sa ido daga Kungiyar Tarayyar Afirka ta AU da kungiyar kasashen yammacin Afrika ECOWAS sun yaba da yadda aka gudanar da zaben Najeriya, cikin kwanciyar hankali ba tare da an samu tashin hankali ba.

Wani na Kada kuri'a shi a zaben Najeriya
Wani na Kada kuri'a shi a zaben Najeriya REUTERS/Kunle Ajayi
Talla

Waikilai 84 kungiyar Tarayyar Afrika ta AU ta aiko, domin sa ido zaben yayin da ECOWAS ta turo da wakilai 250.

A rahotan da kungiyar ECOWAS ta fitar, ta yaba da yadda jama’a suka yi hakuri da juna tare da gudanar da zaben cikin Lumana, sai dai kuma kungiyar ta nuna damuwarta akan yunkurin sace akwatin zabe a wasu rumfuna zaben musamman a Jihar Sokoto, da kuma tashin hankalin da ya yi ajalin wasu mutane a Jihohin Flato da Bayelsa da Yobe.
Kungiyar AU ta jinjina wa Mata akan rawar da suka taka a zaben na Najeriya.

“Mun lura da cewa zabe ya tafi da kyau duk da dai ba zamu ce bisa dari ba, lura da cewar akwai ‘yan matsaloli akan abin da ya shafi Na’urar Card reader amma duk da haka zaben Najeriya abin koyi ne”, a cewar Kwamishiniyar kula da harakokin siyasar kungiyar AU Hajiya Aishatu Laraba Abdullahi.

Kungiyoyin ECOWAS da AU sun yi kira ga manyan ‘yan takarkarin shugaban kasa guda 2 da su amince da sakamakon zaben, tare da kuma ba su shawarar shigar da kara na duk wani korafi da suke da shi ga hukumomin shari’a a kasar.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.