Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan Boko Haram sun bude wa masu zabe wuta a Nafada

Akalla mutane biyu sun mutu a wasu hare hare da Mayakan Boko Haram suka kai a runfunan zabe a kauyukan Birin Bolawa da Birin Fulani cikin karamar hukumar Nafada a Jihar Gombe. Rahotanni sun ce ‘Yan bindigar sun bude wuta bayan an fara tantance masu kada kuri’a.

Jami'an zabe a kan hanyarsu ta zuwa mazabar da aka tura su a Jihar Bayelsa.
Jami'an zabe a kan hanyarsu ta zuwa mazabar da aka tura su a Jihar Bayelsa. REUTERS
Talla

Wani Jami’in Zabe da ya tsira da ransa ya ce ya ji ‘Yan bindigar da jaddada gargadin Kungiyar Boko Haram na a kauracewa runfunan zabe.

A watan jiya Shugaban mayakan Boko Haram Abubakar Shekau ya fito a cikin wani bidiyo yana cewa za su dagula lamurran zabe a Najeriya.

Rahotanni sun ce da misalin karfe 8: 30 agogon Najeriya ne ‘Yan bindigar suka bude wuta a Birin Bolawa bayan an fara tantance masu kada kuri’a tare da kona kayan zabe.

Najeriya na gudanar da zaben shugaban kasa ne da na ‘Yan Majalisu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.