Isa ga babban shafi
Najeriya

Ana zaben Shugaban kasa a Najeriya

Najeriya kasar da ta fi yawan al’umma a Nahiyar Afirka na gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘Yan Majalisun Tarayya a zaben da ya ke daukar hankalin ‘yan kasar da ma kasashen duniya.

Ana tantance masu kada kuri'a a Rumfar Zabe a Dandago Jihar Kano Najeriya
Ana tantance masu kada kuri'a a Rumfar Zabe a Dandago Jihar Kano Najeriya RFI HAUSA/Abubakar Dandago
Talla

‘Yan takara 14 ne ke fafatawa a zaben shugaban kasa.

Amma zaben ya fi jan hankali tsakanin Shugaba Goodluck Jonathan na Jam’iyyar PDP mai mulki da tsohon shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari na babbar Jam’iyyar adawa ta APC.

Wannan ne karon farko da Jam’iyyar PDP mai mulki ke fuskantar babban kalubale a tarihin zaben Najeriya.

Masu sharhi game da siyasar Najeriya sun ce tun kawo karshen mulkin soja a 1999, shekaru 16 da suka gabata ba a taba samun zaben da Jam’iyyar PDP mai mulki ke fuskantar babban kalubale irin wannan karon ba.

Da misalin karfe 8 na safe ne aka soma tantance masu kada kuri’a, kafin a fara jefa kuri'a a misalin karfe 12 na rana.

‘Yan Najeriya kusan Miliyan 70 ke da ‘yancin kada kuri’a a zaben.

Goodluck Jonathan da ke neman wa’adi na biyu zai jefa kuri’arsa ne a mahaifarsa Utuoke yankin kudancin Jihar Bayelsa a kudancin Najeriya

Tsohon shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari zai jefa kuri’arsa ne a garin Daura Jihar Katsina a arewacin Najeriya.

Tuni aka tantance Janar Muhammadu Buhari da misalin karfe 8:45 a mazabar Unguwar yara garin Daura Jihr Katsina.

Masu sa ido a zaben sun kunshi wakilai daga Kungiyar Tarayyar Turai da Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Afrika da kungiyoyin fararen hula.

Ana sa ran samun sakamakon zaben sa’o’I 48 bayan an rufe runfunan zabe, kamar yadda hukumar zaben ta bayyana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.