Isa ga babban shafi
Faransa

An fara tattara bayanai dangane da hatsari jirgin saman Jamus

Kwararru da kuma jami’an tsaro sun ci gaba da bincike  inda jirgin saman Germanwings ya fadi a cikin yanki mai tsaunuka dake kudancin FaransaWata Majiya dake gudanar da bincike kan hadarin jirgin Germanwings da ya hallaka mutane 150 ta ce daya daga cikin matuka jirgin baya kan kujerar sa lokacin da hadarin ya auku. 

Wasu masu  bicinke a Faransa bayan faduwar Jirgin Airbus  na kasar Jamus
Wasu masu bicinke a Faransa bayan faduwar Jirgin Airbus na kasar Jamus
Talla

Bayanan da aka samu daga cikin na’urar nadin Magana ta nuna cewar an tura kujerar daya daga cikin matukan baya, kafin daga bisani akaji kwankwasa kofa sai kuma akaji shiru kafin faduwar jirgin.

Majiyar tace anji kararrawar dake nuna cewar jirgin yayi kusa da kasa kafin faduwar sa, amma kuma babu wani neman taimako daga matukan.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.