Isa ga babban shafi
Najeriya

INEC za ta yi zaben gwaji a Jihohi 12

Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya za ta gudanar da zabukan gwaji a gobe Assabar domin gwada ingancin amfani da na’uran tantance ma su kada kuri’a a Jihohi 12 da a ka zabo daga shiyoyi shida na kasar. Hukumar zaben tace ta tura da na’urar zaben a sassan na Najeriya.

Shugaban Hukumar Zaben Najeriya Farfesa Attahiru Jega
Shugaban Hukumar Zaben Najeriya Farfesa Attahiru Jega
Talla

Jahohin sun hada da Ekiti da Lagos a yankin kudu masu yammaci da Anambra da Ebonyi a kudu maso gabaci da Delta da Rivers a Kudu maso kudu da Kano da Kebbi a arewa maso yammaci da Bauchi da Taraba a yankin arewa maso gabaci sai kuma Nasara da Niger a arewa ta tsakiya.

Ahmed Aminu Manu ya aiko da karin bayani a cikin rahoton da ya aiko daga Abuja.

01:31

Rahoto: INEC za ta yi zaben gwaji a Jihohi 12

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.