Isa ga babban shafi
Chadi

Shugaban Chadi ya bukaci Shekau ya mika kansa

Shugaban Kasar Chadi Idris Deby ya sha alwashin murkushe kungiyar Boko Haram tare da yin kira ga Shugaban Abubakar shekau ya mika kansa, kafin su halaka shi.  Deby ya fadi haka ne a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai bayan ya gana da shugaban Jamhuriyar Nijar Muhammadu Issofou a fadarsa a birnin Ndjamena.

Shugaban Chadi Idriss Deby
Shugaban Chadi Idriss Deby Photo AFP / Bertrand Guay
Talla

Deby ya ce sun san inda Shekau ke buya don haka suna yin kira ya mika kansa kafin su halaka shi kamar yadda aka kashe mayakansa.

Deby ya ce Shekau ya tsere daga garin Dikwa bayan dakarun Chadi sun kwace ikon garin.

Shugaban Mayakan Boko Haram Abubakar Shekau.
Shugaban Mayakan Boko Haram Abubakar Shekau. AFP

Shugaban ya sha alwashin cewa dakarun kasarsa da Nijar za su murkushe kungiyar Boko Haram duk da shaci-fadi da kafofin yada labarai ke yi akai.

Rundunar Sojin Chadi tace Mayakan Boko Haram 117 Dakarun kasar suka kashe a Chadi amma an kashe Soja biyu.

Tuni Nijar da Kamaru da Chadi da ke bakwabta da Najeriya suka kaddamar da yaki domin kawo karshen Mayakan Boko Haram da ke yin barazana ga kasashen na yammacin Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.