Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

MDD zata dauki mataki akan Sudan ta kudu

Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da wani daftari da Amurka ta gabatar game da daukar matakin kakabawa bangarorin da ke rikici takunkumi a kasar Sudan ta kudu bayan sun ki mutunta yarjejeniyar zaman lafiya da suka amince.

Salva Kiir, Shugaban kasar Sudan ta Kudu
Salva Kiir, Shugaban kasar Sudan ta Kudu REUTERS/Tiksa Negeri
Talla

An nada kwamiti da zai yi nazarin sunayen mutanen da za a kakabawa takunkumin wadanda suka hana samar da kwanciyar hankali a kasar. Amma Gwamnatin Sudan ta kudu ta yi gargadin cewa matakin zai lalata yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin bangaoririn da ke rikici.

Masu shiga tsakani a Tarayyar Afrika sun ba Shugaba Salva Kiir da tsohon mataimakinsa Reik Machar wa’adi zuwa Alhamis su cim ma yarjejeniya domin kawo karshen rikicin kasar na tsawon watanni 14 da ya lakume rayukan dubban mutane.

Cikin watan Disamban shekarar 2013, kasar Sudan ta Kudu ta shiga rikici, lokacin da fada ya barke tsakanin dakarun shugaba Salva Kiir da ‘yan tawaye masu biyayya ga abokin adawar shi Riek Machar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.