Isa ga babban shafi
Namibia

Pohamba na Namibia ya lashe kyautar Mo Ibrahim

Shugaban Kasar Namibia Hifikepunye Pohamba ya lashe kyautar Gidauniyar Mo Ibrahim da ake ba shugabannin da suka gudanar da shugabanci na gari da kuma aiwatar da demokiradiya a Nahiyar Afirka. Shugaban mai shekaru 79 da ke shirin barin karagar mulki zai karbi kyautar Dala miliyan 5.

Shugaban Namibia Hifikepunye Pohamba
Shugaban Namibia Hifikepunye Pohamba AFP PHOTO / Stéphane de Sakutin
Talla

Sai dai kuma wasu ‘yan rajin karee hakkin dan Adam a Namibia, na ganin Pohamba, bai cancanci lashe kyautar ba.

Phil Yanangolo babban daraktan wata kungiyar kare hakkin bil’adama yace shugaban bai cancanci ya lashe kyautar ba idan aka yi la’akari da halin kuncin da mutanen Namibia ke ciki, musamman bangaren lafiya da Ilimi da muhalli.

Amma Farfesa Habu Muhammad na Jami’ar Bayero ya ce Shugaban ya cancanci lashe kyautar saboda shugabanci na gaskiya da adalci da ya shinfida a kasar.

Hifikepunye Pohamba, shi ne na hudu da ya lashe kyautar bayan kaddamar da ita a 2007.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.