Isa ga babban shafi

Mayakan Boko Haram sun far wa kauyukan jihar Borno

Mayakan kungiyar Boko Haram sun kai samame a wasu kauyukan da keda iyaka da kasar Kamaru a yankin arewa maso gabashin Nigeria, bayan da sojojin kasar Chadi suka musu luguden wuta a wuraren da suka boye. Rahotannin dake fitowa daga yankin na cewa mayakan, dauke da manyan makamai sun kai munanan hare hare a kan kauyukan dake yankin Kalan-Balgea jihar Borno, inda suka yi ta harbi, tare da daddatsa mutanbe da adda.Wani mazaunin yankin yace maharan suna far wa kauyukan ‘yan Shuwa ne, da suke kabila daya da akasarin sojojin na Chadi. 

Wasu Sojojin kasar Chadi suna bakin aiki
Wasu Sojojin kasar Chadi suna bakin aiki RFI/Madjiasra Nako
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.