Cote d'Ivoire
Matar Gbagbo ta yi watsi da tuhumar da ake ma ta
Matar Tsohon shugaban kasar Cote d’Ivoire Simone Gbagbo ta ki amincewa da tuhumar da ake ma ta na taimakawa wajen tashin hankalin siyasar da aka samu a kasar a lokacin da mijinta ya ki sauka daga mulki bayan an kada shi a zabe. Kasar Cote d’Ivoire ta ki mika matar tsohon shugaban kasar ga kotun duniya da ke neman ta ruwa ajallo inda ta amince a yi ma ta shari’a a gida.
Wallafawa ranar:
Talla
Ana tuhumar Simone da hannu wajen tashin hankalin da ya yi sanadiyar kashe mutane 3,000 da ke adawa da mijinta Laurent Gbagbo wanda yanzu haka ya ke tsare a hannu kotun duniya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu