Dubban Mutane sun kauracewa gidajensu a Afrika ta Tsakiya
Dubban mutane ne, suka kauracewa gidajensu a ‘yan kwanakinnan, sakamakon tarzomar da ke cigaba da tsananta a jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta sanar kenan.
Wallafawa ranar:
Jama’ar sun kauracewa gidajensu ne, dan tsoron salwantan rayukansu sakamakon farmakin ‘yan tawaye da kuma ke yiwa mata fyade bayaga fashin da suke yi a gidajen al-umma.
Tun a farkon shekarar nan, kimanin mutane dubu 30 ne suka kauracewa gidajensu, inda suka nemi mafaka a wasu wuarare cikin kasar ta Afrika Tsakiya, yayinda da kuma, wasu dubu 20 dabam, suka shiga kasar jamhuriyyar Congo da ke da makwabataka da su, dan samun mafaka
Mai magana da yawun hukumar kula da yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya, Karin De Gruiji ya bayyana wa manema labarai a birnin Geneva cewa, akwai tsantsan rugujawar doka da oda a kasar Afrika ta tsakiya, kuma yawan al-ummar kasar ya ragu da kusan rabi.
Kasar dai, na fafutukar farfadowa daga matsalar da ta samu a shekara ta 2013, bayan juyin mulkin da akayiwa Francois Bozize.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu