Isa ga babban shafi

Kungiyar ISIS ta dauki alhakin hari a ofishin jakadancin Iran dake Libya

Cikin wani sakon da suka sanya ta shafin Twitter, mayakan kungiyar ISIS sun dau alhakin kai tagwayen hare haren Bom a gidan jakadan kasar Iran da ke birnin Tripoli na kasar Libya. Bayan kai harin a jiya lahadi Jami’an tsaron Libya sun ce babu wanda ya jikata a harin, wanda shine na baya bayan nan a jerin hare haren da ake auna jami’an diplomasiyya a birnin na Tripoli, kamar yadda Mai magana da yawun hukumomin tsaron kasar Issam Al-Naass ya tabbatar wa kamfanin dilanci labarann Faransa na AFPTuni gwamnati kasar Iran tayi Allah wadai da harin, tare da neman tattaunawa da bangarorin siyasar kasar Libyan, don kawo karshan ta’adanci a kasar kamar yadda mai magana da yawun ministan harkokin wajen kasar Marzieh Afkham ta fadi.Afkham ta kuma ce Iran bata amince kasashen waje su rinka tsoma baki akan harkokin Libya ba, kasar da ake bawa hammata iska tsakanin bangarori dake rikici da juna, lamarin da ya sa aka kafa gwamnati haddin kan kasakasashen duniya da dama sun rufe ofisoshin jakadan cin su a birnin na Tripoli, tun cikin shekarar 2014, lokacin da rikicin ya barke tsakanin kungiyoyin ‘yan bindiga. 

Wasu makamai da aka kwato daga wajen mayakan ISIL
Wasu makamai da aka kwato daga wajen mayakan ISIL REUTERS
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.