Isa ga babban shafi
Chadi-Najeriya

Boko Haram ta kaiwa dakarun Cadi hari

Sojan Cadi uku ne suka mutu a wani hari da yan kungiyar Boko Haram suka kai a arewaci Kamaru a wata sanarwa daga rudunar Cadi a jiya.

Dakarun Cadi a iyakar Kamaru da Najeriya
Dakarun Cadi a iyakar Kamaru da Najeriya AFP PHOTO / ALI KAYA
Talla

Harin da yan kungiyar Boko Haram suka kai ya raunata sojin Cadi 12 yayi da a cewar wanan majiya dakarun Cadi sun samu nasarar kashe mayakan na Boko Haram 123.
Dakarun Cadi sun iso arewaci Kamaru  tun ranar 17 ga watan Janiru da ya shude da nufin kai dauki zuwa rudunar tsaro Kamaru wajen yakar  kungiyar Boko Haram.
Cadi ta tura da kusan sojin 2500 zuwa Kamaru yayi da ake sa ran wasu daga sauren kasashen Afrika za su kasancewa a cikin wanan ruduna ta musaman domin yakar Boko Haram.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.