Isa ga babban shafi
Najeriya

Ba zamu dage lokacin zabe ba-Jega

Shugaban hukumar Zabe mai zaman kanta a Najeriya Farfesa Attahiru Jega ya jaddada cewa ba za su dage lokacin da suka shirya gudanar da babban zabe ba a watan gobe, duk da hukumar na fuskantar kalubale na kammala ba ‘Yan kasar katin zaben na dindin.

Shugaban Hukumar Zabe a Najeriya Farfesa Attahiru Jega
Shugaban Hukumar Zabe a Najeriya Farfesa Attahiru Jega RFI/Bashir
Talla

Tuni dai Jam’iyyar adawa ta APC ta yi watsi da kalaman Mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan sha’anin tsaro Sambo Dasuki, wanda ya ce sun ba hukumar Zaben kasar shawara ta dage zaben shugaban kasa da na ‘Yan Majalisu,  don ba wasu ‘yan kasar damar mallakar katin zabe da kuma matsaloli na tsaro a kasar.

Amma a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a Abuja, Shugaban hukumar Zabe Attahiru Jega yace babu wani zancen dage zaben tare da jaddada cewa hukumar a shirye ta ke ta gudanar da zaben Shugaban kasa da na ‘yan Majalisu a lokacin da aka tsara.

Jega ya ce yana da yakinin za su kammala bayar da katin zabe na dindin ga wadanda ba su karbi katin ba kafin ranar zabe 14 ga watan Fabrairu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.