Dakarun Kamaru sun ceto mutane 24 daga hannun Boko Haram
Hukumomin Kasar Kamaru sun tabbatar da ceto mutane 24 daga cikin 80 da kungiyar Boko Haram ta sace a Arewacin kasar. Wannan na zuwa ne a yayin da Chadi ke shirin kaddamar da yaki akan Mayakan.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Sojojin Kamaru sun kora Mayakan na Boko Haram zuwa Najeriya bayan kwashe lokaci suna musayar wuta da su a arewacin kasar.
Wani Sojan Kamaru ya shaidawa Kamfanin Dillacin labaran Faransa cewa ‘Yan Boko Haram sun kai hari ne a wasu kauyuka guda biyu a yankin arewa mai nisa tare da sace mutane 80. Wannan ne kuma karo na farko da Boko Haram ta sace mutane a wata kasa sabanin Najeriya.
Kasar Chadi tace zata aika da dakaru 400 da jirage masu saukar Ungulu domin yakar Boko Haram a arewacin Kamaru.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu