Isa ga babban shafi

An sake koran wasu Ministoci 7 a kasar Zimbabwe

Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe, ya kori ministoci 2 da mataimakan ministoci 5, a ci gaba da kokarin kakkabe abukan kawancen tsohuwar mataimakiyarsa Joice Mujuru, da yake yi daga cikin gwamnatin kasar. Mr. Mugabe, da a halin yanzu yake hutu a yankin yamma maso gabashin kasar, ya kori ministan dake kula da tafiya, da harakokin fadar shugaban kasa, da kuma na ofishin mataimakinsa, bisa dalilan rashin iya aiki kamar yadda fadar shugaban kasar ta sanar Har ila yau shugaba Mugabe ya salami mataimakan ministan kiyon lafiya, na shari’a raya karkara, kwadago da kuma na sufuri.Daukacin ministocin 7 an alakantasu ne da zama ‘yan koren korarar mataimakiyar shugaban kasar, uwargida Joice Mujuru ne, wace Shugaba Mugaben ya kora tare da wasu ministoci 7, a ranar 9 ga watan Disamba da muke ciki, bayan korata daga cikin jam’iyarsa ta Zanu PF mai mulkin kasar ta Zimbabwe.An jima dai ana daukar korariyar mataimakiyar shugabar kasar ta Zimbabwe uwargida Joice Mujuru, a matsayin wace zata gaji tsohon shugaban kasar ta Zimbabwe dan shekaru 90 a duniya.Mugaben na kan karagar shugabanci kasar, tun cikin shekarar 1980 sakamakon zarge zargen da aka yi mata na rashin iya aiki, cin hanci da rashawa, da kuma kokarin hada baki da ita wajen yinkurin hallaka shugaba Mugabe. 

Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe
Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.