Isa ga babban shafi
Sudan

An dage ranar zaben gama gari na kasar Sudan

Hukumar zaben kasar Sudan ta dage ranar gudanar da zabubuka a kasar, domin bai wa Majalisar Dokoki damar yi wa kundin tsarin mulkin kasar gyran fuska, lamarin da zai bai wa shugaba Omar Albashir damar nada gwamnoni ba tare da an gudanar da zabe ba. A yanzu dai hukumar zaben ta bayyana cewa za a gudanar da zabubukan ne a ranar 13 ga watan Afrilun shekara mai zuwa ta 2015, yayin da aka karawa ‘yan takarar lokacin da za su gabatar da bukatarsu ta tsayawa a zabubukan, daga ran 31 ga wannan wata na disamba zuwa 11 ga watan Janairu mai zuwa.Shugaban hukumar zaben Mukhatar Hassan Al-Assam, ya bayyana wa manema labarai cewa a halin yanzu ba za su iya tabbatar da cewa za a gudanar da zaben gwamnoni a kasar ba, domin kuwa abu ne mai yiyuwa Majalisar dokoki ta yi wa kundin tsarin mulkin gyra kafin ranar zaben.Tuni dai jam’iyyun adawa suka bayyana rashin amincewarsu da wannan dama da majalisar ke neman bai wa shugaba Albashir, yayin da wasu daga cikin jam’iyyun adawar suka soma yin kira ga magoya bayansu da su kaurace wa zaben.Zaben shubancin kasar dai zai kasance na biyu daga lokacin da Albashir ya dare karagar mulkin kasar, shekaru 25 da suka gabata. 

Shugaban Sudan Omar Hassan Al Bashir
Shugaban Sudan Omar Hassan Al Bashir
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.