WHO
Ebola ta kashe mutane 7, 373
Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce adadin mutanen da cutar Ebola ta kashe a Afirka ta Yamma ya tashi zuwa 7, 373. Hukumar tace rahotan da ta ke da shi zuwa ranar 16 ga watan nan ya nuna cewar mutane 19,031 suka kamu da cutar a kasar Guinea da Liberia da Saliyo, kuma 7.373 suka mutu daga cikin su.
Wallafawa ranar:
Talla
Sauran kasashen da aka samu cutar kuma aka samu rasa rayuka sun hada da Mali inda mutane 6 suka mutu da Amurka idan aka samu mutuwar mutum guda sai kuma Najeriya inda mutane 8 suka mutu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu