Isa ga babban shafi
Guinea

Conde ya yi gargadin barazanar Boko Haram a Afrika

Shugaban Kasar Guinea Alpha Conde ya yi gargadin cewar rikicin Mayakan Boko Haram na iya mamaye yankin yammacin Afrika idan har kasashen yankin ba su dauki matakan bai-daya ba wajen murkushe Boko Haram. Conde wanda ke ziyara a kasar Faransa ya ce muddin aka samu matsala a wata kasa kuma suka kasa hada kai domin ganin an magance matsalar to tana iya yaduwa zuwa wasu kasashe.

Shugaban kasar Guinée Alpha Condé.
Shugaban kasar Guinée Alpha Condé. AFP PHOTO / CELLOU BINANI
Talla

Shugaban yace rikicin Najeriya da yanzu ya shiga Kamaru gobe yana iya tsallakawa kasashen Nijar da Chadi da Mali har zuwa kasarsa ta Guinea.

Conde ya ce akwai bukatar kasashen Afrika su kai wa Najeriya dauki domin kawo karshen ayyukan Boko Haram.

Kungiyar Boko Haram ta kashe mutane sama da 13,000 a arewacin Najeriya tare da tursasawa sama da Miliyan guda da rabi gujewa gidajensu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.