Isa ga babban shafi
Najeriya

Ebola: An warkar da Dan Najeriya a Holland

Mahukuntan kasar Holland sun ce an yi nasarar warkar da wani Sojan Majalisar Dinkin duniya Dan asalin Najeriya daga cutar Ebola, bayan an shigo da shi kasar domin samun magani. Wata Cibiyar binciken lafiya a kasar tace Dan Najeriyar ya warke bayan an shigo da shi kasar a ranar 6 ga watan Disemba.

Jami'an lafiya suna aikin kawar da Ebola a Monrovia kasar Liberia
Jami'an lafiya suna aikin kawar da Ebola a Monrovia kasar Liberia © Sébastien Nemeth
Talla

Sojan wanda ke aikin wanzar da zaman lafiya, ya kamu da Ebola ne a kasar Liberia, nan take ne kuma aka nufi kasar Holland da shi domin kula da lafiyarsa.

Cutar Ebola dai ta kashe mutane kimanin 6,900, yawanci a kasashen Liberia da Saliyo da kuma Guinea.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.