Isa ga babban shafi
Najeriya

An yanke wa Sojojin Najeriya 54 hukuncin kisa

Kotun Sojin Najeriya ta yankewa wasu sojoji 54 hukuncin kisa bayan samunsu da laifin cin amanar kasa. Birgediya Janar Mohammed Yusuf ne ya shugabanci kotun a Abuja birnin Tarayya. An samu sojojin 54 da laifuka biyu da suka hada da laifin yunkurin bore da kuma aikata boren.

Sojin Najeriya da ke yaki da Mayakan  Boko Haram
Sojin Najeriya da ke yaki da Mayakan Boko Haram AFP PHOTO/ PIUS UTOMI EKPEI
Talla

Sojoji sun fito ne daga runduna ta bakwai da ke Maiduguri mai yaki da kungiyar Boko Haram, kuma kotun ta bukaci a harbe su baki daya.

Sojojin sun hada da kofur guda biyu, masu igiya daya guda 9 da kuma kurata 49.

Kotun tace a ranar 4 ga watan Agusta ne sojojin da ke runduna ta bakwai suka yi bore, tare da bijirewa aikinsu.

Lauya Femi Falana ne ya wakilci sojojin da aka yanke wa hukuncin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.